Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bukaci Turkiyya Da Ta Yi Taka Tsantsan


Sakataren harkokin waje John Kerry yace Amurka na goyon bayan a hukumta wadanda suka yi yunkurin juyin mulki, amma kuma bai kamata Turkiyya ta yi amfani da wannan lamarin wajen gallazawa masu yin adawa da ita ba.

A yau Litinin Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce ya na goyon bayan a hukunta wadanda suka yi yunkurin juyin mulki a Turkiyya, sai dai ya yi gargadin cewa ya kamata gwamnati ta yi taka-tsantsan domin kada ta wuce gona da iri, yayin da ta ke kokarin maido da doka da oda.

“Muna tare da gwamnatin Turkiyya,” amma kuma muna kira ga gwamnatin ta Turkiyya da ta kwantar da hankulan mutanen kasar baki daya.” In ji Kerry bayan wata ganawa da ya yi da takwarorinsa na kungiyar tarayyar turai a Brussels.

Kerry ya kuma yi kira ga gwamnatin da ta bi tsarin doka na mutunta cibiyoyin dimokradiyya, inda ya kara da cewa lallai su suna goyon bayan a hukunta masu laifi, amma kuma kada a wuce gona da iri wajen hukunta masu hanu a yunkurin juyin mulkin.

Kafofin yada labarai mallakar gwamnati sun ruwaito cewa ya zuwa yanzu an dakatar da jami’ai 8,777 kana ana tsare da wasu 6,000 daga bangaren shari’a da na soji, bayan yunkurin juyin mulkin na ranar juma’a, lamarin da ya sa kasashen duniya suka nuna ya kamata a yi taka-tsantsan domin kada a ruguza ginshikan da suka tsaida doka da oda a kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG