Da ya ke magana da manema labarai jiya Alhamis a Paris, babban birnin kasar Faransa, Francois Molins ya ce bayanan da suka samu na hotuna da binciken da ya yi a wayar salularsa, na nuna cewa tun daga shekarar 2015 ya fara shiri.
Molins ya ce wasu mutane biyar da a yanzu ake zargi sun shiga hannu su na fuskantar mataki na farko na zargin aikata ta'addanci, ciki har da hada baki don aikata kisa da kuma mallakar makamai, da kuma rawar da su ka taka wajen taimakawa mutumin ya aikata ta'addancin na ranar 14 ga watan Yuli.
Ya ce mutane hudu ne ake zargi biyu Faransawa 'yan asalin kasar Tunisiya, da wani dan Tunisiya da wani dan Albaniya, da wata mata mai takardar izinin zama 'yar Faransa da kuma Albaniya a lokaci guda. Hukumomin Leken Asirin Tsaron kasa ba su san da su ba a baya, a cewar kafar labaran Faransa ta AFP.
Mutumin da ya abka da motar, Mohammed Lahouaiej Bouhlel, dan shekaru 31, dan asalin kasar Tunisiya ne da ya zauna a Nice na tsawon shekaru.