Kungiyar tsofaffin ‘yan Sanda a Najeriya, ta bukaci Gwamnatin tarayya da ta duba tsarin biyan kudin sallama da fansho da akewa ‘ya’yan ta dan su samu rayuwa mai inganci.
A wani taro da tsofaffin ‘yan Sandan daga jihohi daban daban na fadin taryyar Najeriya, suka gudanar a Jos fadar Gwamnatin jihar Filato.
Tsofaffin ‘yan Sandan sunkoka yadda wasu kamfanoni dake biyan su kudin sallama da fansho ke yi masu wulakanci kafin su biya su kudin fansho da bai taka kara ya karya ba.
Kungiyar ta tsofaffin ‘yan Sandan ta bakin Sakataren ta ASP, mai ritaya Silvanus Basadinbo, ta bukaci Gwamnati da tayi gyara akan kudaden sun a fansho dan suma su tafi bai daya da sauran jama’a.
Wasu daga cikin tsofaffin ‘yan sandan sun koka da yadda aka baiwa kamfanoni kudadensu domin sarrafawa amma idan suka bukaci koda bashi ne sai abun ya gagara.