Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sun ki Amincewa da Takardan da Ofisoshin Jakadancin Nijar Suka Kirkiro


‘Yan Siyasa magoya bayan Jam’iyyun hamayya a Jamhuriyar Nijar mazauna arewacin Najeriya, sun gudanar da wani gangami a karamin Ofishin jakadancin Jamhuriya Nijar dake Kano, domin nuna rashin amincewa da wata takarda da ofisoshin jakadancin kasar suka kirkiro cewa sai da ita ne ‘yan Nijar mazauna kasashen waje, zasu sami damar kada kuri’a a yayin babban zaben kasar, da ake sa ran zai gudanarwa a cikin watan Disambar bana.

Daruruwan magoya bayan jam’iyyun hamayya kimani goma sha bakwai daga jamahuriyar Nijar, din ne suka gudanar da taron gangamin a nan Kano suna masu nuna kin jinin yunkurin ofishin jakadancin na samarda wata takarda da hukumomin suka ce lalle sai duk wani dan jamhuriyyar masaunin kasashen waje ya mallaketa ne zai iya jafa kuri’a a yayin zabe.

Fitattu daga cikin jam’iyyun sun hada da MNSD Nasara, CDS Rahama da kuma jam’iyyar Lumana da dai sauransu.

Malam Abdullahi, shugaban hadakar jam’iyyun hamayyar wanda kuma ya jagoranci gangamin yace “ Idan kana da takarda zama dan kasa, ko kana da fasfo ko takardan haihuwa ko takardan haraji da kake biya a garinku ko kuma idan kai tsohon ma’aikaci ne za’a baka takardan rajista.”

Ya kara da cewa ” ‘yan uwan mu na Lagos sun yi wannan kira akan wannan yada zango da ake yi ta bayan gida basu daina ba shine yasa muma muka hada namu gangamin domin fadawa duniya cewa ga abin da Ofisoshin jakadancin keyi bamu yarda da takardan ba.” Abunda muke ji tsoro yasa bamu so ayi shine saboda Jaki da Doki ma za’a basu takardan tunda babu sheda zuwa za kayi da farar takarda kawai a rubuta maka cewa kai dan Nijar ne.”

Wakilin muryar Amurka Mahmud Kwari ya nemi ji ba’asi daga Ofishin jakadancin kasar ta Nijar a Kano hakan bai samu ba.

XS
SM
MD
LG