Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Bata Kashi Tsakanin Fulani da Gwarawa


Manuma
Manuma

Mutane ukku sun rasa rayukansu a wani bata kashi da aka yi a tsakanin Fulani Makiyaya da kabilar Gwarawa manoma a kauyen Lawo dake yankin karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Ricikin dai ya tilastawa daruruwan manoma Gwarawa, tserewa daga gidajen su inji hakimin yankin , Alhaji Tanko Baba Kuta, yana mai cewa “Yanzu mutanen mu lalle Fulani sun koresu daga gidajensu yanzu haka fiye da mutane dari biyu suna harabar makaranta a Maikunkele a garin Minna inda suke gidun hijira.”

Mataimakin shugaban kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya, Alhaji Hussaini Bosso, wanda ke cikin masu shiga tsakani domin sasanta wannan tashin hankali yace “ Karamar Magana ce ta sama babba kan maganar banna wanda aka saba akan burtali, ya sama shi manomi bai yi hakuri bay a dauki doka a hannun ya kai ga harbi ya sama a sanadiyar wanna Bafulatani daya ya rasa ransa sannan manoma biyu suka rasa nasu rayukan.

Rikicin Fulani makiyaya da manoma dai na kara ta’azzara a jihar Neja, inda ko ranar lahadin da ta gabata an yi wani tashin hakalin a tsakanin Fulani da ‘yan banga a yankin Lambata dake cikin karamar hukumar Gurara, wanda yayi sanadiyar mutuwa mutane hudu.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Bala Elkana, yace yanzu haka rundunar na rike da ‘yan banga guda ukku akan rikicin na Lambata., domin gudanar da bincike, akan rikicin yankin karamar hukumar Shiroron kuwa yace shima suna gudanar da bincike akai, amma a daya gefen kuma suna ganawa da shugabanin bangarorin domin fadakar dasu mahimmancin zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG