Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rage Ma'aikatan Aikin Hajjin Bana


Makka
Makka

Gwamnatin jihar Neja, ta rage yawan ma’aikatan dake kula da Alhazai a kasa mai tsarki, wadanda zasu gudanar da aikin Hajji a bana.

Mataimakin Gwamnan jihar wanda kuma shine Amirul Hajjin bana na jihar Muhammad Keso, yace rashin kudi shine dalilin rage ma’aikatan .

Hukumar jindadin Alhazan jihar ta Neja, tace har yanzu tana ci gaba da neman wani jami’in hukumar da yayi sama da fadi da makudan kudaden Alhazan jihar a shekarar da ta gabata.

Shine dai wannan jami’in hukumar Alhazan dake kula da karamar hukumar Bosso, mai suna Ahmed Bala Barkuta a bara ne ya tsere da sama da Naira miliyan asahirin da takwas na maniyyatan karamar hukumar Bosso da suka biyar ta hannun sa kuma har ya zuwa wannan lokaci babu labarinshi.

Hajiya Rabi Datijo kwamishiniyar hukumar mai kula da tsare tsare tace hukumar tayi iyakacin kokarinta amma haka bata cimma ruwa ba.

Amma tace an sayarda motocin sa kuma an sa gidan da ya malaka a kasuwa, har yanzu ba’a samu mai saye ba.

XS
SM
MD
LG