Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayern Munich ta Saye Dan Wasan Tsakiya na Juventus Arturo Vidal


Dan wasa Arturo Vidal
Dan wasa Arturo Vidal

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kammala sayen dan wasan tsakiya na Juventus, Arturo Vidal, a kan kudi kimanin Euro miliyan 40, ko dala miliyan 44, watau fiye da Naira miliyan dubu 9 da 600. A makon jiya zakarun wasannin lig-lig din na Jamus suka ce sun kammala cimma yarjejeniya da kungiyar Juventus, abinda kawai ake jira shine likitoci su duba lafiyar Vidal, idan sun ga yana da koshin lafiya sai ya sanya hannu kan yarjejeniyar komawa Bayern Munich.

Ran litinin da maraice Vidal mai shekaru 28 ya sauka a Munich, kuma jiya talata likitocin suka duba shi suka kuma ce zai iya was aba tare da matsala ba.

Vidal ya fadawa shafin Bayern Munich na intanet cewa wannan wani sabon babi ne a rayuwarsa, kuma yana fatan zai yi kokari yayi fice a nan. Zan yi kokarin taimakawa Bayern ta lashe wasanni, in ji shi.

Bayern ta shiga kasuwa neman dan wasan tsakiya a bayan da Bastian Schweinsteiger ya koma Manchester United a baya cikin watan nan. A can baya, Bayern tayi kokarin sayen Vidal a shekarar 2011 lokacin yana kulob din Bayer Leverkusen, amma sai ya zabi komawa Juventus a lokacin.

Vidal mai shekaruy 28 da haihuwa ya taimakawa kasarsa Chile wajen lashe kofin zakarun kasashen nahiyar Amurka ta Kudu watau Copa America a bana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG