Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata ga Maganin Kishiya ga Masu Bukata


Mata kyawawa
Mata kyawawa

Malama Habiba wata matashiya ce mai sana’ar saida kayan gyaran jiki ga ‘yan mata. Wadannan kayan sunadarin datake saidawa suna taimakawa wajen maida tsohuwa matashiya, wannan sunadarin nata anasamosu ne daga itatuwa, don kara nagartar jiki da lafiyar ‘yanmata.

Ta fara wannan sana’ar tatane a matsayin ‘yar aike, amma daga bisani sai taga yakamata itama ta fara nata. Takan karbi wadannan kayan gyaran jikin don sayarwa sai su raba ribar da mai ainihin kayan, wanda tahaka tasamu nata sana’ar, kuma tana samu alkhairi matuka.

Idan har mata sun yi amfani da wanna sunadarin nata ta yadda yakamata, to lallai bashakka zai taimaka musu wajen gyaran fatarsu harma da jawo hankalin mazajensu, da wasu kale-kalle.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG