Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Nada Tsohon Jami’in Shige Da Fice Tom Homan A Matsayin Mai Kula Da Kan Iyakoki


Tsohon Darekta na ICE) Tom Homan
Tsohon Darekta na ICE) Tom Homan

Da yammacin jiya Lahadi, zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai dawo da jami’in kula da shige da ficen nan mai ra’ayin rikau Tom Honan ya zama mai kula da kan iyakokin kasar a gwamnati mai shigowa.

“Ina mai farin cikin shaida cewa tsohon darakta a hukumar kula da shige da fice da yaki da fasakwabri, kuma jigo a harkar kula da kan iyakoki, Tom Homan, zai shigo cikin gwamnatin Trump, a matsayin mai kula da kan iyakokin kasarmu”, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na “Truth Social”.

Donald Trump a West Palm Beach, Florida
Donald Trump a West Palm Beach, Florida

“Na san Tom da jimawa, kuma babu wanda ya fi shi a harkar sa idanu da kula da kan iyakokinmu.”

Trump ya bayyana cewa Homan zai kula da harkar “tasa keyar bakin haure zuwa kasashensu na asali”.

Dan jam’iyyar Republican mai shekaru 78 ya sha alwashin kaddamar da aikin tasa keyar bakin haure mafi girma a tarihin Amurka-a ranar farko ta hawansa kan karagar mulki.

Ya yi ta nanata kyamarsa game da yin kaura ta baranauniyar hanya yayin yakin neman zabensa, inda ya rika amfani da kausasan kalamai akan mutanen da suka “gurbata jinin” Amurka.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG