Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Ce An Tuhume Shi Da Laifin Kwasar Wasu Takardun Bayanan Sirri


Trump Classified Documents
Trump Classified Documents

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ana tuhumarsa da laifin karkatar da wasu takardu na sirri da aka gano a gidansa da ke Florida.

WASHINGTON, D.C. - Trump ya bayyana haka ne a dandalinsa na sada zumunta 'Truth Social", lamarin da ya haifar da tuhumar gwamnatin tarayya da za a iya cewa ita ce bazanar shari’a mafi tsananin da aka yi wa tsohon Shugaban yayin da kuma yake neman komawa fadar White House.

Trump ya ce an bukace shi da ya bayyana a kotun Tarayya ta Miami ranar Talata da karfe uku na yamma. Amma ya ce "BAN AIKATA LAIFI BA" .

Trump
Trump

Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ba ta yi wani karin bayani ko kuma tabbatar da batun ba a halin yanzu.

Dama mataimakansa suna cikin shiri kan yuwuwar tuhumar shi a binciken bayanan sirri da ake gudanarwa, yayin da aka hango masu gabatar da kara da ke gudanar da binciken a yau Alhamis a wata kotun Miami inda babban alkalai ke sauraron bahasi daga bakin shaidu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG