Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump Zai Gurfana Gaban Kotun Tarayya


Tsohon shugaban Amurka Donald Trump yayin da ake hawa jirginsa zuwa birnin Miami don gurfana gaban kotu.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump yayin da ake hawa jirginsa zuwa birnin Miami don gurfana gaban kotu.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya isa kulob din Golf dinsa da ke birnin Miami gabanin gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zarginsa da laifin karkatar da wasu bayanan sirrin tsaron kasar bayan ya bar fadar White House a shekarar 2021.

An shirya gurfanar da Trump da karfe uku na rana a ranar Talata, kuma za a yi zaman cikin tsauraran matakan tsaro a cikin wata kotun tarayya da ke cikin garin Miami.

Hukumomin tarayya sun kara tsaurara matakan tsaro a kusa da ginin kotun, kuma jami'an Miami sun ce a shirye suke don hana duk wani tashin hankali daga magoya bayan Trump da masu adawa da shi.

"A cikin garinmu, a fili yake mun yi imani da Kundin Tsarin Mulki kuma mun yi imanin cewa ya kamata mutane su sami 'yancin bayyana ra'ayoyinsu," in ji magajin garin Miami Francis Suarez a wani taron manema labarai. “Amma kuma mun yi imani da doka da oda. Kuma mun san hakan, kuma muna fatan gobe za a yi zaman lafiya.”

Shari’ar Trump na zuwa ne kwanaki biyar bayan da masu taya alkali na tarayya yanke hukunci a Miami suka amince da tuhumarsa da laifuka 37, ciki har da tuhume-tuhume 31 da ke zarginsa da “rike” bayanan sirrin kasa wanda ya saba wa dokar leken asiri.

An kuma tuhumi wani mai taimaka wa Trump, Walt Nauta da laifin kawo cikas ga yunkurin gwamnati na karbo takardun.

Trump shi ne tsohon shugaban kasa na farko da ya fuskanci tuhumar gwamnatin tarayya. Wannan dai shi ne karo na biyu cikin watanni biyu da ake tuhumar sa.

Tsohon shugaban na fuskantar tuhume-tuhume daban-daban na aikata laifuka a birnin New York dangane da kashe makudan kudi ga wata babbar jarumar fina-finan batsa yayin yakin neman zabensa na 2016.

A zaman na ranar Talata, alkali zai sanar da Trump hakkinsa tare da karanta tuhume-tuhumen da ake masa. Ana sa ran zai amsa ba shi da laifi.

Yawancin lokaci, ana gabatar da kara a ranar da aka kama mutum. Sai dai bisa la’akari da yanayin shari’ar Trump da ba a taba yin irinta ba, an dage zamansa na farko a kotu na tsawon kwanaki biyar.

An dai mika karar ne ga mai shari'a Aileen Cannon, wacce Trump ya nada wadda ta sha suka saboda fifita tsohon shugaban a hukuncin da ta yanke a shari'ar a bara.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG