Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Yan Majalisar Wakilan Amurka Na Ci Gaba Da Kokarin Ganin Sun Tsige Shugaba Biden


Zaman sauraron bahasin tsige shugaban Amurka.
Zaman sauraron bahasin tsige shugaban Amurka.

'Yan jam'iyyar Republican a Majalisar Wakilan Amurka na ci gaba da kokarin ganin an kada kuri’a a wannan makon, wadda za ta tabbatar da binciken tsige Shugaba Joe Biden. Sai dai babu tabbas kan ko shugabanni na da isassun kuri'u don amincewa da matakin.

Da yuwuwar za a iya kada kuri’a ‘yan kwanaki kadan, sabon binciken jin ra’ayin mutane da aka fitar da safiyar Litinin ya nuna cewa wasu ‘yan kadan daga cikin Amurkawa ne su ka yi imanin cewa ya kamata a ci gaba da gudanar da binciken, amma ko a tsakanin ‘yan Republican da ke da alaka da junansu, sha’awar binciken na kara yin baya.

Binciken da wani kamfani mai suna Morning Consult ya gudanar, ya nuna cewa kashi 44 cikin 100 na Amurkawa sun yi imanin cewa, ya kamata a ci gaba da binciken, idan aka kwatanta da kashi 40 cikin 100 da suka yi imanin bai kamata ba.

Sakamakon ya karya lagon bangaranci, inda kashi 62 cikin 100 na 'yan Democrat, suka ce bai kamata a ci gaba da binciken ba, yayin da kashi 70 cikin 100 na 'yan Republican suka ce ya kamata.

Yawancin masu zabe da basu da alaka da wata jam’iyya kashi 47 cikin 100, sun ce bai kamata a ci gaba da binciken ba, inda 37 cikin 100 suka ce ya kamata.

A karkashin dokar Amurka, ana iya tsige shugaban kasa daga mukaminsa ba tare da wani tsarin zabe ba, idan Majalisar Dattijai ta same shi da laifin "cin amanar kasa, ko cin hanci ko wasu manyan da munanan laifuka." Binciken tsigewa shine matakin farko na tsarin da zai kai ga ci gaba da tsige shi a Majalisar, kuma idan aka yi nasara, za a yi shari’a a Majalisar Dattawa.

Yayin da tsigewar ba ta da yawa a tarihi, Amurkawa suna da gogewa kan wannan batu da ya faru a baya-bayanan. An tsige tsohon shugaban kasar Donald Trump sau biyu a wa'adin mulkinsa.

A cikin 2019, an tsige shi saboda matsin lamba ga shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, da ya kaddamar da bincike kan Biden, sannan ake ganin zai iya yi wa Trump hammaya a zaben shugaban kasa na 2020.

An sake tsige shi a karo na biyu a shekarar 2021, bayan yunkurin da ya yi na soke sakamakon zaben shugaban kasa na 2020, wanda ya haifar da harin da aka kai kan ginin Majalisar Dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairu.

dukkan shari’o’in biyu, an wanke Trump a Majalisar Dattawa, inda ake bukatar kashi biyu bisa uku na masu rinjaye don ci gaba da yanke hukunci.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG