Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Sami Goyon Bayan Manyan 'Yan Republican


TRUMP-ACUSACIONES-VISTAZO
TRUMP-ACUSACIONES-VISTAZO

Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar Rifabulikan da ke hamayya da neman zaben fidda gwanin na Trump sun caccaki zargin samun Trump da laifi.

'Yan sa'o'i bayan samun tsohon shugaban Amurka da laifin wofintar da muhimman takardun sirri na tsaro a Florida, manyan 'yan jam'iyyar Rifabulikan a Washington sun fito da shafukansu na yanar gizo su na mara baya ga Trump din da zigin amfani da doka ba bisa ka'ida ba a bangaren gwamnatin Joe Biden.

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump
Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump

Kakakin majalisa Kevin McCarthy, wanda shi ne mafi tasirin a 'yan Rifabulikan a Washington, ya fito a shafinsa na tiwita ya nuna rashin amincewa da cajin da aiyana shi da "abunda ba daidai ba" yanda gwamnatin Biden za ta dau mataki kan na kan gaba a zaben fidda gwani na Rifabulikan da zai yiwu ya kalubalanci Biden a zaben shugaban kasa a badi.

Kakakin majalisa Kevin McCarthy
Kakakin majalisa Kevin McCarthy

Ko da wasu daga cikin 'yan jam'iyyar Rifabulikan da ke hamayya da neman zaben fidda gwanin na Trump sun caccaki zargin samun Trump da laifi.

Gwamnan Florida Ron DeSantis ya ya yi watsi da cajin da zaiyana shi da amfani da gwamnati a matsayin makami kamar yanda magoya bayan tsohon shugaban kan yayata kalamin.

Gwamnar Florida Ron DeSantis a
Gwamnar Florida Ron DeSantis a

Shugabannin jam'iyyar Rifabulikan sun ci gaba da nuna goyon baya ga Trump a yammacin jiya jumma'a tun bayyana cajin 37 da su ka hada da 31 da su ka shafi rike takardun sirri da gangan, caji daya na neman katsalandan ga lamuran shari'a, caji hudu da su ka shafi boye bayanan sirri sai kuma caji daya da bayanan karya da canja bayanai.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG