A jiya Alhamis ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ra’ayin sa game da yadda za a mallaki bindiga a makarantu.
Yace yana so ya zamanto kashi 20 zuwa 40 na malaman makaranta da suka samu horaswa sosai ne kawai zasu mallaki bindiga a boye cikin makarantu domin dakushe irin hare-haren da ake kaiwa a makarantu.
A lokacin da yake amsa wata tambayar VOA a karshen wani taron tattaunawar mintoci 55 akan irin yadda ake harbe-harbe a makarantu, a fadarsa ta White House, shugaba Trump yace, "malaman da suke so ne kawai za a ba bindigar. Kashi kadan kawai cikinsu zasu samu, amma suna da yawa. Da zarar an yi haka, nan take irin wannan bala'in zai kawo karshe."
Trump yace daga yanzu zai tabbatar sai an gudanar da binciken kwa-kwaf ga duk wani wanda zai sayi bindiga, haka kuma za a daga shekarun mallakar ta daga shekaru 18 zuwa 21, sannan za a haramta sayar da wani irin inji da ake makalawa jikin bindiga domin kara mata saurin fitar da harsasai.
Yace ba shakka muna son mu tabbatar cewa anyi wani abu game da wannan lamari, Shugaban na Amurka ya fadawa jami'an gwamnati dama sauran jama'ar gari haka ne sailin ganawar da yayi da su a fadar White House ta gwamnatin Amurka yace ba abinda yafi kare yaran mu muhimmanci.
A cikin sakonsa na farko a shafin Twiter shugaba Trump yace muddin aka horas da wasu malamai yadda zasu sarrafa bindiga, wannan zai basu damar mayar da martani nan take ga masu mummunar tabi'ar kai hari a cikin makaranta, haka kuma wannan zai zamo wata hanyar samar da tsaro.
Facebook Forum