Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Daga Kanmu Ba Za A Sake Kai Hari A Wata Makarantar Amurka Ba," Inji Wata Daliba


Emma Gonzalez lokacin da ta ke magana.
Emma Gonzalez lokacin da ta ke magana.

A cigaba da mai da martani kan hare-haren da ake kai wa makarantu a Amurka, wata dalibar makarantar da aka kai hari na baya-bayan nan, ta lashi takobin ganin cewa daga kansu ba za a sake kai hari kan wata makanranta ba.

“Za mu zama na karshen ganin harbin kan mai uwa da wabi,” kudurin da Emma Gonzalez ta yi Kenan, wadda ta tsallake rijiya da baya a harbin kan mai uwa da wabin da aka yi a Makarantar Sakandaren Marjory Stoneman Douglas a jahar Florida. Gonzalez ta yi wannan kudurin ne yayin da ta ke magana a wani gangamin kiran a tsai da wanzuwar bindiga a jiya Asabar, kwanaki uku bayan da wani tsohon dalibin makarantar ya bindige ‘yan ajinsu Gonzalez su 17 da kuma wata malama.

Gonzalez ta yi magana gabanta-gadi ga masu sauraronta, wadanda daruruwan mutane ne da su ka taru a harabar kotun tarayya ta Fort Lauderdale, mai tazarar kilomita 45 daga inda harin ya auku.

Gonzalez ta ce matsalar tabin hankali – wadda ita ce Shugaba Donald Trump da sauran hukumomi kan danganta da harbe-harben – ba ita ce babban sanadi ba; ta dora laifin kan rashin tsaurin dokar bindiga ta Florida, wadda a karkashinta ne wannan matashin maharin mai suna Nikolas Cruz ya sayi makaman na shi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG