Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Bincike Na Musamman Ya Kara Tuhumar Mutane Biyu Da Suka Yiwa Trump Kemfen


Robert Mueller, mai bincike na musamman
Robert Mueller, mai bincike na musamman

Jiya Alhamis Robert Mueller mai binciken katsalandan da ake zargin Rasha da yiwa zaben Amurka na shekarar 2016 ya kara tuhumar Manafort, tsohon shugaban kemfen din Donald Trump, da mataimakinsa Gates, da laifuka 32

A jiya alhamis ne mai bincike na musamman, Robert Mueller, ya gabatarwa da kotu takardun karin tuhuma a kan tsohon shugaban yakin neman zaben shugaba Trump, wato Paul Manafort, da wani jami'in yakin neman zaben na Trump mai suna Richard Gates.

Tuhume-tuhumen da a yanzu suka kai har 32, sun karu da wata tuhumar kin biyan haraji, da aikata zamba don karbar rance a banki. Da ma tun fari an tuhume su da laifuffukan batar da sawun kudade, sai kuma kin yin rajista a matsayin wakilin kasar waje dangane da ayyukan da suka yi na kare muradun 'yan siyasa masu goyon bayan kasar Rasha a Ukraine.

Sabbin laifuffukan da ake zargin sun aikata sun hada da cewar tare da taimakon Gates, Manafort ya batar da sawun kudi fiye da dala miliyan 30 ta hanyar rarraba su a cikin wasu bankuna na kasashen waje, ya kuma yi amfani da wannan dukiya da ya boye wajen gudanar da rayuwa irin ta bushasha anan Amurka ba tare da biyan kudin haraji na wadannan kudaden da yake samu ba.

Dukkansu biyu dai sun batar da sawun kudaden da suka samu daga ayyukansu a Ukraine da cewa basussuka ne, domin su kaucewa biyan haraji kan kudaden. Haka kuma an yi zargin cewa sun gabatar da takardun neman basussuka ga bankuna, inda suka kara yawan kudaden da suke samu na zahiri domin bankunan su ji dadin ba su rance.

Takardar tuhumar ta ce sunyi anfani da wadannan kudaden wajen sayen gidaje, tare da kawata wadanda suke dasu, yayin da shi ko Gates yayi amfani da wasu bangaren kudin nasa ne wajen biyan kudin makarantar yaransa.

Manafort da Gates sun ki amsa laifuffukan farko da aka tuhume su da aikatawa a watan Oktoba na 2017.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG