Donald Trump wanda shi ne yake kan gaban 'yan takarar jam'iyyar Republican a fafutikar fidda gwani da ake yi yanzu ya iso nan Washington DC inda ya gana da wasu kusoshin jam'iyyarsa dake cikin majalisun dokokin kasar.
Yayinda ya gana dasu ya bayyana sunayen wasu da zai sa su zama masu bashi shawara akan harkokin waje da dai makamantansu.
Ya zo ne ya kawar da shakkun da wasu suke dashi a kansa musamman akan dangantakar kasar da Israila da kuma manufofinsa na siyasa kasancewa ba dan siyasa tsantsa ba ne shi.
Can baya Trump wanda yake ji da kansa ya kauracewa birnin Washington DC fadar gwamnatin Amurka saboda yadda yake yawan zagin sauran 'yan takarar jam'iyyarsa da 'yan majalisun da suke ganin ba zai yi nisa ba a zaben fidda gwani amma sai gashi yana kan gaba.
Yawancin 'yan jam'iyyar dake da ra'ayin rikau, ba duka ba, suna kokarin su yi masa zagon kasa su hanashi samun nasara duk da cewa yana kan gaba a zaben fidda gwani.
Trump ya lissafa sunayen mutane biyar da suka hada da Sanata Jeff Sessions daga jihar Alabama wani mugun makiyin bakin haure da zasu bashi shawara akan harkokin waje.