Dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump, wanda yake kan gaba ga sauran 'yan takarar su 16 a kuri'ar neman jin ra'ayin 'yan Republican, ya soke halaratar wani taron da wata kungiya mai ra'ayin rikau ta shirya a jihar Carolina ta kudu, jiya jumma'a, a dai dai lokacinda yake fuskantar suka ta ko ina saboda ya gaza gyara ikirarin da wani mai goyon bayansa yayi cewa, "shugaban Amurka Barack Obama musulmi ne, kuma ma ba dan Amurka bane.
Kwamitin yakin neman zaben Mr. Trump yace dan kasuwar yana gudanar da wasu muhimman shawarwari ta fuskar kasuwanci wanda bai samu ya kammala ba ranar Alhamis, shi yasa ba zai halarci taron ba.
Abokanan takararsa suna taboshi kan wannan batu.
Tun a maraicen Alhamis, Trump ya fada cikin wannan rikici, lokacinda yake yakin neman zabe a birnin Rochester, dake jihar New Hampshire.
Mutumin yace, muna da matsala a kasan nan, sunan matsalar "musulmi", inji mutumin wanda yake saye da sigileti na masu goyon bayan Mr. Trump.Ya ci gaba da cewa mun san shugaban kasarmu na yanzu yana cikinsu. Kuma kasan bama ba Amurke bane.
Mutumin da yake goyon bayan Trump ya kara da cewa "akwai sansanonin da suke karuwa nanan, inda su (musulmin) suke shirin ko suke son su kashe mu. Itace tambayata "Yaushe ne zamu kawarda su"?
Ba-ma Mr. Trump bai gyarawa mutumin ksukurern da yayi ko ya soki ikirarin da ba dai dai bane cewa shugaba Obama musulmi ne, haka nan ya gaza tunkarar abunda wasu da dama suka fassara a matsayin kira na kora ko kuma gamawa da duk musulmi da suke Amurka.