Trump ya gayawa shirin tashar talabijin ta CNN cewa Iraqi ta zama tamkar jami'ar "Harvard a kaurin suna amma wajen ta'adanci".
"ana fille kawunan mutane. Ana halaka su cikin ruwa. Yanzu haka rayuwar a kasar tafi tsanani idan aka kwatantada da zamanin da Saddam Hussein ko Gaddafi suke muki a kaashensu' Inji Donald Trump.
Trump yace Gabas ta Tsakiya ta "rude," karkashin shugabancin shugaba Obama da kuma sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, babbar abokiyar hamayyarsa a neman shugabancin Amurka.
Haka nan Trump wanda shine akan gaba tsakanin masu neman Jamaiyyar Republican ta tsaida su takarar shugabancin Amurka ya zargi tsohon shugaban Amurka George Bush saboda harin mamaya da Amurka ta kai kan kasar Iraqin a shekara ta 2003. Rahotanni da gwamnatin Bush ta yi anfani dasu har ta mamaye Iraqi basu da kanshin Gaskiya. Zargin cewa kasar tana da makaman kare dangi ba Gaskiya ba ne.