A daren Litinin ne, Trump ya tada rigima a ciki da wajen Amurka lokacinda ya bada shawarar a hana musulmi shiga Amurka. Amma duk da hakan zuwa jiya Alhamis, sakamakon neman jin ra'ayoyin jama'a a fadin Amurka da kuma a wasu wurare da za'a fara zaben,ya nuna farin jinisa sai karuwa yake yi.
Kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a na baya bayan nan da tashar talabijin ta CBS da jaridar New York Times suka gudanar a fadin Amurka bai daya ya nuna Trump yana kan gaba da kashi 35 cikin dari, can gaba da Senata Ted Cruz daga jihar Texas wanda yake da kashi 16 cikin dari, sai kuma tsohon likitan kwakwalwa Ben Carson d a kashi 13 cikin dari. A kuri'ar da aka yi a jihohi, Trump yana can kan gaba a jihar New Hampshire, yayinda yake gogayya da Ted Cruz a jihar Iowa, a jihar South Carolina kuma, yana kan gaba.
A nata kuri'ar neman jin ra'ayin jama' data gudanar, tashar talabijin ta FOX tace sakamakon ya nuna Trump da kashi 35 cikin dari, sai kuma mai bi masa tsohon likita Dr. Ben Carson da kashi 15 cikin dari, sannan Ted Cruz da Marco Rubio sunyi kunnen doki da kashi 14 ko wanne daga cikinsu.