Yau Alhamis, Papa Roma Francis, ya tsoma kansa cikin siyasar Amurka, inda yayi nuni da cewa mutumin da yake kan gaba a jerin masu takara shugabanci watau Donald Trump ba "Kirista ba ne", saboda shawarar da ya bayar na gina babbar ganuwa kan iyakar Amurka da Mexico ta kudancinta domin hana bakin haure tsallakowa cikin Amurka.
Shugaban darikar katholikan yayi wannan furucin ne kan hanyarsa ta komawa Roma bayan ziyarar da ya kawo Mexico cikin makon nan, har ya jagoranci addu'a ta musamman abainar dubban jama'a jiya Laraba, kusa da kan iyaka da jihar Texas, zangon galibin bakin haure masu zuwa daga Mexico da sauran kasashe dake Latin Amurka.
Trump wanda dan darikar Presbitarian ne wanda yake yakin neman zabe a jihar Carolina ta kudu, yace kalaman Papa Roman ba "kalamai ne da suka dace ba."
Yace "shakkun da Papa Roma ya nuna kan addininsa abun takaici ne"