Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Jam’iyyar Democrat Da Donald Trump Na Jam’iyyar Republican Suke Kan Gaba


Wanna sakamakon bai zo da mamaki ba. Saboda zaben jin ra’ayi da aka yi ya nuna cewa Trump da Clinton ne zasu yi nasara

Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrat da Donald Trump na jam’iyyar Republican sun kara jaddada matsayinsu na ja-gaba a kokarin neman zamowa ‘yan takarar shugaban kasar Amurka na jam’iyyunsu, a bayan da suka samu manyan nasarori a wasu muhimman jihohin da suka jefa kuri’un tsayar da ‘yan takara jiya talata, ranar da ta fi kowacce muhimmanci a kakar tsayar da ‘yan takara a Amurka.

Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Clinton ta lashe jihohin Tennessee, Alabama, Georgia, Virginia, Arkansas, Texas da kuma Massachusetts. Shi kuma abokin hamayyarta a jam’iyyar ta Democrat, Bernie Sanders mai ra’ayin gurguzu, ya lashe jihohin Vermont, Oklahoma, Minnesota da Colorado.

A bangaren ‘yan jam’iyyar Republican kuma, Trump ne ya lashe jihohin Arkansas, Tennessee, Georgia, Alabama, Virginia, Vermont, da Massachusetts. Shi kuma sanata Ted Cruz ya sami nasara a jihohin Texas da Oklahoma da Alaska, sanata Marco Rubio shi kuma ya sami nasararsa ta farko a jihar Minnesota.

Wanna sakamakon bai zo da mamaki ba. Saboda zaben jin ra’ayi da aka yi ya nuna cewa Trump da Clinton su za su yi kan gaba a zaben na jiya Talata.

XS
SM
MD
LG