Cruz ya doke Donald Trump da maki goma sha biyar, kamar yadda sakamakon farko ya nuna, wanda Cruz ya bayyana a matsayin nasarar ‘sauya akala da kuma kiran hadin kai ga Amurka. Dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Texas ya kuma maida hankali kan tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, yana buga kirji cewa zai lashe zabe ba na zama dan takarar jam’iyar Republican kadai ba, amma harda babban zabe na kasa da za a gudanar a watan Nuwamba.
Yace, bari in ce Hillary, Ki shirya. Gamu nan tafe.
Trump bai yi bayani a bainar jama’a ba bayan rufe runfunan zabe jiya da dare, sai dai kamfen dinsa ya fitar da sanarwa yana caccakar Cruz da kakkausan lafazi da cewa, masu neman su hana a tsaida Trump takara a babban taron jam’iyar da za a gudanar a Cleveland cikin watan Yuli ne a jam’iyar suke iza shi.
Sanders mai wakiltar jihar Vermont a majalisar dattijai kuma ya doke Clinton da kashi 55 cikin dari a zaben da aka gudanar a Winsconsin. Yanzu ya lashe jihohi shida daga cikin bakwai da aka gudanar zabe a baya bayan nan, ya kuma shaidawa magoya baya a Wyoming da zasu gudanar da nasu zabe ranar Asabar cewa, kamfen dinsa ya himmatu.
Clinton ita ma bata yi jawabi ba bayan kammala zaben a Wisconsin. Sai dai ta taya Sandars murna a shafinta na twitter ta kuma gayawa magoya bayanta “gaba dai”.