Jam'iyyar Republican zata yi taron kolin ne a cikin watan Yuli inda lokacin ne zata gudanar da zabe tsakanin wakilan da aka zaba su zabi wanda zai tsaya takarar shugaban kasa da sunan jam'iyyar Republican.
Zaben fidda gwani da aka yi a jihar Wyoming ranar Asabar da ta gabata ya kara karfafa shakkun da ake dashi cewa dole sai an je taron koli kafin a san wanda zai tsaya saboda Ted Cruz shi ya samu duk wakilai 14 na jihar.
To saidai duk da nasarar da Cruz ya samu a Wyoming ana kyautata zaton hamshakin attajirin nan Donald Trump shi ne zai lashe zaben fidda da gwani da za'a yi gobe Talata a jihar New York da gagarumar tazara. Idan hakan ya faru attajirin zai kara samun wakilai kan wadanda yake dasu yanzu.
Duk da cewa attajirin yana da wakilai da dama Ted Cruz yana kokarin jawo hankalin wasu wakilan attajirin zuwa wajensa da zummar zasu zabeshi idan an je taron koli maimakon shi Trump.
Wannan kokari na Cruz ya sa Trump yana zargin ana yi masa magudi domin a hanashi samun nasara karfi da yaji.
Shugabannin jam'iyyar Republican sun msanta zargin magudi da Trump ya yi suna cewa dokokin jam'iyyar da tsarinta sun dade da kafuwa, ba tun yau suke ba kuma su ne za'a yi anfani dasu.
A bangaren jam'iyyar Democrats Hillary Clinton zata samu isassun wakilai da zasu sa ta zama zakarar jam'iyyar saidai idan Sanders mai hamayya da ita ya lashe duk sauran wakilan lamarin da yanzu yana da wuya.