WASHINGTON, D. C. - A wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya jajantawa iyalan marigayin, Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Delta, da gwamnati, da kuma al’ummar jihar baki daya.
Shugaban ya kuma yi murna da irin tasirin rayuwar marigayin, wanda kuma fitaccen farfesa ne a fannin likitanci, tare da amincewa da irin shawarwarinsa na zaman lafiya a tsakanin 'yan Najeriya da kuma rawar da ya taka wajen neman kulla kawance a tsakanin ‘yan kasar mai makon rarrabuwar kawuna.
“Mai martaba ya yi cikakken rayuwa da aka ayyana ta mai girman akidar zaman lafiya, hadin kai, kishin kasa, gaskiya, da mutunci. Wannan babban rashi ne, yana zuwa a daidai lokacin da Najeriya ke bukatar karin masu samar da zaman lafiya da gina kasa,” in ji Tinubu.
Ya bukaci Iyalan sarkin da duk wadanda ke bakin cikin wannan rashi da su jajanta da irin tasirin da Mai Martaba Sarki ya bari.
Dandalin Mu Tattauna