Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadan Najeriya A Morocco Mansur Nuhu Bamalli Ya Rasu


Mansur Nuhu Bamalli
Mansur Nuhu Bamalli

Allah ya yi wa Jakadan Najeriya a kasar Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli rasuwa yana da shekara 42.

Marigayin wanda har zuwa rasuwarsa shi ne Magajin Garin Zazzau, ƙani ne kuma ga Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli.

Wata sanarwa da jami’in yada labarai na Masarautar Zazzau ya fitar a ranar Juma’a ta ce Ambasada Bamalli ya rasu ne a daidai lokacin da ya ke kan shirin zuwa kasar Moroko a yau Jumma’a kammar yadda jaridar Channelstv ta rawaito.

Sanarwar ta kara da cewa za'a sanar da lokacin da za'a yi masa sallar jana’iza daga baya.

Idan ba a manta ba, a baya tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada marigayin a matsayin jakadan Morocco a shekarar 2022.

Kafin nadin nasa a matsayin jakada, ya rike mukamin mataimakin darakta a ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya.

Alhaji Mansur ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya biyu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG