Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Ma'aikata Na Tarayya A Najeriya Adamu Fika Ya Rasu


Adamu Fika
Adamu Fika

Allah ya yi wa tsohon Shugaban Ma'aikata na Tarayyar a Najeriya Malam Dr. Adamu Fika (Wazirin Fika) rasuwa yana da shekaru 90 a duniya.

Fika ya rasu ne a daren ranar Talata 24 ga watan Oktoba bayan ya dawo daga wani asibiti da ke Landan zuwa wani asibitin da ke a jihar Kaduna a cewar jaridar politics Nigeria.

Marigayi Wazirin Fika, Alhaji Adamu Fika, wanda aka haifa a shekarar 1933 dattijo ne da ake girmamawa a Najeriya kuma gogaggen jami’in gwamnati ne.

A lokacin rayuwarsa ya rike mukamai da dama, ciki har da Shugaban Majalisasr Koli ta Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU), da kuma shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar kare muradun Arewa (ACF).

Za a sallaci gawarsa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a yau Laraba da karfe 4:00.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG