Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Ya Yi Wa Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Ghali Umar Na'abba, Rasuwa


Ghali Na'abba
Ghali Na'abba

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba, ya rasu ne bayan fama da jinya a wani asibiti a Abuja ya na mai shekaru 65.

Allah ya yi wa tsohon kakain majalisar dokokin Najeriya Dr. Ghali Umar Na'abba rasuwa.

Marigayin ya rasu bayan fama da jinya a wani asibiti a Abuja ya na mai shekaru 65.

Ghali Na'abba wanda shaharerren dan siyasa ne ya zama kakakin majalisar wakilan Najeriya bayan dawowa dimokradiyya a 1999 inda ya rike mukamin har zuwa shekara ta 2003.

Masanin kimiyyar siyasa na jami'ar Bayero ta Kano Dr.Sa'idu Ahmed Dukawa ya ce marigayin ya bar tarihin jajircewa a harkokin shugabanci inda ya yi tsayin dakan hana majalisar wakilai zama 'yar amshin shatan sashen zartarwa a wa'adin farko na mulkin Olusegun Obasanjo.

Tuni a ka shiga mika sakon ta'aziyyar rasuwar marigayin wanda haifaffen jihar Kano ne.

Bayanai na nuna za a gudanar da jana'izar a Kano yau din nan Laraba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG