Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Yaba Da Hukunci Kotun Koli Kan Kananan Hukumomi


Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yaba da hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan ‘yancin kananan hukumomi, yana cewa ‘yan Najeriya, musamman talakawa, za su iya tuhumar shugabanninsu.

A hukuncin da kotun kolin ta yanke a ranar Alhamis ta ce ya saba kundin tsarin mulkin kasa gwamnonin su rike kudaden kananan hukumomi.

Kotun Kolin ta kuma hana gwamnoni rushe shugabannin kananan hukumomin da aka zaba bisa tafarkin dimokaradiyya, inda ta ce yin hakan ya saba wa kundin tsarin mulki na shekarar 1999.

Jim kadan bayan yanke hukuncin, shugaban ya ce rashin ingantaccen tsarin gudanar da kananan hukumomi babban kalubale ne ga ci gaban al’ummar kasar tsawon shekaru.

A cikin wata sanarwa da ya fitar kakakin fadar shugaban Najeriya Ajuri Ngelale, ya ruwaito Shugaba Tinubu na cewa “saboda wannan hukunci, mutanen mu, musamman talakawa, za su iya tuhumar shugabannin yanki kan ayyukan da suka yi da kuma wadanda ba su yi ba.

Ya ce “Za’a san abin da ake aikawa a asusun kananan hukumomi, kuma yanzu dole ne a samar da ayyuka ba tare da uzuri ba.”

Sanarwar ta kara da cewa “Gwamnatina ta shigar da wannan karar saboda imanin da muke da shi cewa dole ne mutanen mu su sami sauki kuma hukunci da aka yanke a yau zai tabbatar da cewa wadannan kananan hukumomi ne da jama’a su ka zaba kawai za su kula da kudaden jama’a.”

Ya ce hukunci da kotun kolin ta yanke na tabbatar da ‘yancin da tsarin mulki ya bawa kananan hukumomi dangane da ‘yancin cin gashin kai na sarrafa kudade da sauran muhimman ka’idoji, yana da matukarmuhimmanci kuma yana kara karfafa kokarin inganta tsarin tarayyar Najeriya don ci gaban kasa baki daya.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa Atoni-Janar na tarayyar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), bisa jajircewa da kishin kasa, inda ya bayyana shari’o’in a matsayin wani muhimmin aiki.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG