Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni kan Mafi Karancin Albashi


Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu

Mataimakin shugaban kasar ne ya jagoranci taron da gwamnonin jihohi da mataimakan gwamnoni da ministoci kafin isowar shugaban kasar.

A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Bola Tinubu da mataimakin sa Kassim Shettima suka gana da gwamnonin jihohi 36 na tarayyar kasar tare da ministoci, inda suka tattauna kan batun sabon mafi karancin albashin ma’aikata, da ma sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.

Shugaban kasar da gwamnonin sun gana ne a taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) karo na 141, wanda ya gudana a zauren majalisar dokoki da ke Abuja, babban birnin kasar.

Taron na ranar Alhamis ya zo ne kimanin kwanaki biyu bayan da Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta yi watsi da batun sake duba mafi karancin albashin ma’aikata.

A ranar Laraba ne gwamnonin karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) suka yi taro a Abuja inda suka tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago za su samar da ingantaccen albashi.

Shugaban Tinubu a jawabinsa na ranar dimokradiyya a ranar 12 ga watan Yunin 2024 ya tabbatar wa kungiyar kwadagon cewa nan ba da jimawa ba za a aika da wani kudirin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa ga majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG