Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mafi Karancin Albashi: Tinubu Zai Gana Da Hadaddiyar Kungiyar Kwadago


Hakan na zuwa ne kimanin wata gudu bayan da Shugaba Tinubu ya sanarda cewar zai aikewa majalisar kasa kudirin akan mafi karancin albashi domin zartarwa.

Shugaban Kasa Bola Tinubu zai gana da hadaddiyar kungiyar kwadago a Abuja a gobe Alhamis domin cigaba da tattaunawa akan mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya.

Hakan na zuwa ne kimanin wata gudu bayan da Shugaba Tinubu ya sanarda cewar zai aikewa majalisar kasa kudirin akan mafi karancin albashi domin zartarwa.

Wata babbar majiyar ‘yan kwadago ta shaidawa tashar talabijin ta Channels cewar, shugaban kasar ya gayyaci shugabannin kungiyar kwadago ta NLC da takwarorinsu na TUC zuwa ganawar da ake sa ran zata wakana a fadar Aso Villa dake birnin Abuja.

Ana sa ran shugaban kasar ya yanke matsaya akan tayin Naira dubu 62 da bangaren gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu suka gabatar da kuma na Naira dubu 250 da bangaren ‘yan kwadagon ya gabatar.

Taron na ranar Alhamis na zuwa kimanin wata guda bayan da Tinubu a jawabin daya gabatar a ranar dimokiradiya, 12 ga watan Yunin daya gabata, yace nan bada jimawa ba za’a aike da kudiri akan mafi karancin albashi daga bangaren zartarwa zuwa ga majalisar kasa domin a zartar da shi.

A ranar 25 ga watan Yunin daya gabata ne, Majalisar Zartarwa ta Kasa karkashin jagorancin Shugaba Tinubu ta jingine cigaba da nazari da tattaunawa akan batun mafi karancin albashin domin bada damar fadada tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Kwanaki 2 bayan hakan, Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima suka gana da gwamnonin jihohin Najeriya 36 da ministoci akan batun sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar, yayin karo na 141 na taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG