Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Jajantawa Mutanen Da Gobarar Kasuwar Karu Ta Shafa


Bola Tinubu
Bola Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mika sakon jajensa ga ‘yan kasuwar da shaguna da dukiyoyinsu suka kone a gobarar data tashi a kasuwar Karu a daren Alhamis.

Sanarwar da hadimin shugaban kasar akan harkokin yada labarai, Ajuri Ngilale ya fitar a yau Juma’a tace, shugaban kasar yayi takaicin samun labarin gobarar data shafi wani sashe na kasuwar.

Da yammacin jiya Alhamis, gobara ta lakume wani yanki na kasuwar, inda ta lalata dimbin dukiya da sauran kayayyaki masu daraja.

Sanarwar ta kara da cewar, shugaban kasa na mika sakon jajensa ga ilahirin ‘yan kasuwar da wannan mummunan al’amari ya shafa, sannan yana basu tabbacin samun tallafi daga gwamnatinsa.

Shugaban kasar ya kuma yi kira da a rika taka tsantsan da daukar matakan kariya, domin kare afkuwar gobara da sauran bala’o’i anan gaba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG