Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Albashi Mafi Karanci


Lokacin da shugaba Tinubu yake sanya hannu kan dokar albashi mafi karanci a Abuja, Najeriya (Hoto: X/Dada Olusegun)
Lokacin da shugaba Tinubu yake sanya hannu kan dokar albashi mafi karanci a Abuja, Najeriya (Hoto: X/Dada Olusegun)

Tinubu ya sanya hannu a dokar a Fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin a lokacin taron majalisar zartawa da aka saba yi a kowane mako.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinuba ya rattaba hannu kan dokar da ta amince da naira 70,000 a matsayin albashi mafi karanci a kasar.

A makon da ya gabata Majalisar Dokokin kasar ta amince da kudurin dokar wanda za a rika biya a matsayin albashi mafi karanci a kowane wata.

Tinubu ya sanya hannu a kan dokar ne a Fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin a lokacin taron majalisar zartawa da ake yi a kowane mako.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswin Akpabio ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar dokoki a lokacin sanya hannu a wannan sabuwar dokar.

Gabanin amincewa da wannan kudurin doka, an yi ta kai ruwa rana tsakanin kungiyar kwadago da gwamnati kan albashin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG