Maganar tsaro na duniya, matsalar ‘yan gudun hijira da rashin tabbacin siyasa sune manyan abubuwan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da takwarorinsa guda 7 suka fi maida hankali akai, a lokacin da suka kammala zaman rana ta farko a jiya na tattaunawarsu a Japan.
A yayin da taronsu na kwana biyu ke tafe a Hiroshima, birnin da ya jikkata da harin bam din Amurka na Atomic gabanin karewar yakin duniya na biyu. Mista Kerry ne Ministan harkokin wajen AMurka na farko da zai ziyarci wannan birni.
A wata hira da yayi da wata Jaridar birnin na Hiroshima mai suna Chugoku Shimbun, Kerry yace, barazanar da duniya ke fuskanta na bukatar hada hannun duniya don daukar mataki.
Ya kara da cewa, irin wannan muhimmiyar dam ace ke bada ikon yin magana da yawu daya game da tsaro da siyasar duniya don daukar mataki bai daya. Kasashen dai da ke wannan taro dukkansu masu karfin arzikin masana’antu ne da suka hada da Birtaniya, Canada, Faransa, Jamus, Italiya da Japan.