An tsananta matakan tsaro lokacinda Mr. Kerry ya sauka a Paris babban birnin kasar Faransan a daren jiya Litinin. An hana 'yan jarida raka shi, matakin da ake gani shine irinsa na farko ga babban jami'i da ya kai ziyar aiki a fadar wata kasa a Turai.
Yace "kada wani yayi kokwanto har yanzu da hasken fitila tana ci a birnin da ake kira mai haske" inji Mr. Kerry. Yace "yau mu duka 'yan birnin Paris ne."
Tunda farko shugaban kasar Farncois Hollande, ya lashi takobin zafafa kai farmaki a Syria, inda daga can ne aka kitsa makarkashiyar hare haren da aka kai kan birnin. Shugaban ya gabatar da jawabin ba kasafai ba ga hadin gwiwar majalisun kasar.
Haka nan kuma a jiya Litinin, hukumomin kasar suka kama mutane 23 a sumamen da suka kai a duk fadin kasar, suna masu fadin cewa sun gano mutumin da ake zargin shine madugun shirya hare haren da aka kai kan kasar.