Jiya Alhamis ne Mr. Kerry yayi magana a taron shekara shekara na ministocin harkokin waje na kasashen da suke majalisar tsaro ta turai ko NATO. Taron na kwanaki biyu ana yinsa ne a birnin Belgrade na kasar Serbia.
Ranar Laraba Kerry ya ziyarci Kosovo d a Serbia, inda ya gana da manyan jami'an gwamnatin kasashen.
Yanzu kuma nan ba da jumawa ba, mata anan Amurka zasu sami sukunin gudanar da dukkan ayyukan da ada maza kadai ne suke yi a fagen yaki.
Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter ne ya bada sanarwar haka jiya a Alhamis a helkwatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon.
Mata sun juma suna kutsawa tun a wajajen 1970, lokacinda a karon farko aka basu damar shiga makarantun horasda sojoji da kuma shiga aikin soja. A yanzu dai babu sashen da babu mata a rundunar mayakan Amurka illa shiga fagen daga.
Sakataren yace babu yadda za'a yi a wannan karni ace rundunonin mayakan Amurka zasu iya kauda fuska kan rabin al'uma kuma tayi fatar samun ci gaban ayyukanta.