Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki da kungiyar ISIS na kan hanya - John Kerry


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry

Amurka na jagorar kasashen dake kawance da ita akan yaki da kungiyar ISIS wadda tayi ikirarin kafa daular Isalama a yankunan da ta kwace daga kasashen Iraqi da Siriya

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fada yau Talata cewa kokarin da su keyi na murkushe kungiyar ISIS na nan kan hanya kuma yana tafiya daidai kamaryadda aka shirya.

Amma John Kerry ya yi kashedi. Yace dole a tabbatar da dorewar kasashen Libya da Iraqi, a mara masu baya su zama kasashen dake rayuwa cikin zaman lafiya, lumana da walwala.

John Kerry yayi wannan jawabin ne yayinda ake bude taron ministoci daga kasashe 20 da suka hallara a birnin Rome domin lalubo hanyar habaka da inganta yaki da daular Islama da ISIS ke ikirarin kafawa.

Ya jawo hankalin kasashen akan hadarin dake akwai idan har ISIS ta samu ta mamaye Libya wadda take da albarkatun man fetur mai dimbin yawa. Yarjejeniyar da aka cimma na kafa gwamnatin hadin kai zai taimaka kwarai saboda haka dole ne a marawa yarjejeniyar baya ta ci nasara a samu tsayayyar gwamnati.

John Kerry ya kara da jawo hankalin kasashen aka tabarbarewa rayuwa a kasar Siriya. Lamarin ya yi muni kuma ba'a taba ganin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu. Ya kira kasashe su yi magana da kakkausan lafazi domin a tsagaita wuta a samu akai ahajin gaggawa duk inda mutane suka makale.

XS
SM
MD
LG