Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yan Sanda A Kano Ta Kama Mutane Hudu Kan Hari Da Aka Kai A Helkwatar PDP


Ayarin 'Yansandan Najeriya da suke yin sintiri.
Ayarin 'Yansandan Najeriya da suke yin sintiri.

Mutane hudu sun fada hanu kan hari da aka kai helkwatar jam'iyyar PDP.

Wasu mutane dauke da adduna da wukake da sauran muggan makamai sun kai hari sakatariyar reshen jihar Kano na Jam’iyyar PDP, inda shugaban kwamitin riko na jam’iyyar da aka nada daga Abuja ya kaddamar da sauran mambobin kwamitin a makon jiya.

Tuni rundunar 'Yan sandan jihar ta bakin kakakinta ASP Mustapha Abubakar ya tabbar da aukuwar wannan lamari, kuma yace tuni har rundunar ta kama mutane hudu dangane da wannan hari. Kuma suna ci gaba da bincike.

An kai harin ne lokacinda mataimakin shugaban kwamitin riko na jam'iyyar yake taro da wakilan jam'iyyar daga mazabu uku na 'yan majalisar dattijai da suka fito daga jihar domin tsara yadda za'a gudanar da gangamin jam'iyyar domin tarbar shugaba kwamitin riko.

Kakakin yada labaran jam'iyyar ta PDP ya shaidawa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari yadda aka kai musu harin, har aka kusan daba masa wuka, amma Allah ya kare.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG