Gwamna Kwankwaso ya gaya ma wakilinmu da ke Fadar Shugaban Nijeriya a Abuja Umar Faruk Musa
cewa su tara su ka zabi Rotimi Amaechi a matsayin shugaba amma aka yi kokarin dannewa a bai wa wanda ya ci kuri’u 16. Ya ce kuma a jihar Rivers an cire masu shugabanni ba bisa ka’ida ba, sannan sun ce a je a gyara al’amura amma an kasa.
Ya ce ko ga batun sauran abubuwan da su ka shafi tsarin shugabanci da yaki da rashawa. Wannan ma in ji shi an kasa gyarawa. Y ace su a Kano sun a shugabanci ne ta wajen nuna misali. Shi ya sa, in ji shi, a Kano ba wanda zai yi sata hankalinsa kwance.
Dangane da fitar su jam’iyyar PDP karkashin shugabancin Bamanga Tukur kuwa, Gwamna Kwankwaso ya ce makomarsu ta dogara ne kan yadda jama’a su ka so. Y ace a yayin da wasu ke son a kafa sabuwar jam’iyya; wasu kuma so su ke a shiga jam’iyyar APC. Ya ce daga karshe su dai abin da jama’a ke so za su yi.