Gwamna Lamido ya bayyana wannan rahoton a zaman sharri na mahassada wadanda ke ci gaba da kokarin rarraba kawunansu da neman haddasa wata fitina a tsakanin su masu neman kawo sauyi cikin jam'iyyar ta PDP.
A cikin hirar da yayi da Muryar Amurka, gwamna Sule Lamido yace su da suka rungumi wannan tafiya ta ganin an samu sauyi cikin PDP da kuma yadda ake mulki, sun yi haka ne tare da sanin cewa rayukansu da na mukarrabansu da 'ya'yansu da iyalansu duk zasu shiga cikin wani hali, amma duk da haka sun rungumi wannan akidar saboda sun yi imanin cewa gaskiya suka dogara a kai.
Gwamna Lamido ya ce, "saboda wannan kuduri da muka dauka na wannan matsayin namu, mun san za a zo kan matsayin da za a rika bada bayani na karya, da sharfri, a zo a ce wane kaza-kaza. Har ma azo a ce an ba wane mukami kaza, duk wannan abu za a yi domin gwara kawunanmu ne."
Da yake karyata jita-jitar cewa wai gwamna Aliyu babangida ya janye daga PDP-Sabuwa ce domin yana kwadayin wani mukami nan gaba, gwamna Lamido yayi watsi da wannan zancen yana cewa ai "Babangida Aliyu ba yaro ba ne."
Yace shi kansa da Aliyu Babangida, sun fadawa sauran abokan tafiyarsu cewa abin nan da suka shiga, babu makawa a ciki, ko su nutse tare, ko suyi iyo tare, amma ba zasu ja daga kan matsayinsu ba.