Wannan kuwa, ya biyo bayan abinda ta ce "ya kai amfani da sojoji wajen rantsar da daya daga cikin wadanda ke jayayya kan kujerar shugabancin karamar hukumar Madagali."
Wanda aka rantsar kuwa, shi ne Mr. Maina Ularamu, dan takarar PDP na bangaren Bamanga Tukur, wanda jiya litinin kotu ta bayarda umurnin cewa shi ne halaltaccen shugaban karamar hukumar.
Kotun ta soke zaben da aka ce an yi ma Mr. James Abawa Watharda a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP. Shi dai Mr. Watharda, yana goyon bayan gwamna Murtala Nyako da kuma bangaren sabuwar jam'iyyar PDP 'yar santsi karkashin jagorancin Baraje.
Tun fari, Mr. Watharda ya daukaka kara zuwa babbar kotun Jihar Adamawa, wadda ta bayarda umurnin cewa a dakatar da rantsarwar, amma duk da haka aka je aka rantsar da Mr. Ularamu.
A martanin da gwamnatin jihar Adamawa ta mayar kan wannan dambarwar, ta yi zargin cewa wasu su na kokarin kawo fitina a jihar ta hanyar kin bin umurnin kotu.
Ibrahim Abdul’Aziz ya aiko da karin bayani daga Yola.