Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Gano Bakin Zaren Fakewa Da Addini Wajen Aikata Ta’addanci


ABUJA: Adduar karshe ta watan Ramadan a babban Masallacin Najeriya dake Abuja
ABUJA: Adduar karshe ta watan Ramadan a babban Masallacin Najeriya dake Abuja

Malamai daga duk sassan Najeriya sun taru a Abuja don taron gano bakin zaren fakewa da addinin musulunci da wasu miyagu ke yi su aikata ta’addanci.

Taron dai ya gudana ne karkashin jagorancin Sultan Mohammad Sa’ad Abubakar da Asusun raya lamurran ci gaban kasa na MDD wato UNDP.

‘Daya daga malamai daga Kano limamin masallacin Shehu Tijjani, Mohammad Nasiru Adam yace sai an kula da yadda ake aika sakonni a wajen wa’azi. Ya kuma ce ba kowanne malami bane ya kamata a baiwa damar wa’azi har sai an gamsu da fahimtarsa an tabbatar fahimta ce mai kyau.

Sheik Nasir Adam na daga malaman da suka taru a Abuja lokacin da kungiyar JIBWIS da al rabitah al alam islami suka shirya gagarumin taron cusa kyakkyawar akida. Sheik Karibullah Nasiru Kabara, ya nuna damuwar cewa fituna a Najeriya kan faro ne daga karamar ‘kura.

Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG