Anga wata daga matan da jaririnta na wani ‘dan ta’addan Boko Haram, wanda nan take mahaifin yarinyar sanye da jar dara ya ‘dauki jikan nasa a cikin farin ciki da godiyar Allah, dake nuna koma dai me ya faru yarinyar dai ta dawo daga hannun ‘yan ta’addan da ranta.
Da alamu dai har matan 21 dai sun fara murmurewa ta samun sabbin tufafi da abinci mai gina jiki, ba irin ukubar da suka sha hannun ‘yan Boko Haram ba a dajin Sambisa.
Wasu daga cikin iyayen yaran sun nuna farin cikinsu da ganin ‘ya ‘yan nasu raye, wata uwa kuma wadda ‘yar ta bata da ga cikin yaran ita ma ta nuna farin cikinta game da ganin yadda wasu iyaye suka sami ‘ya ‘yansu.
Rahotanni sun ambato shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya yabawa duk wadanda suka taka rawa wajen shiga tsakani har aka cimma yarjejeniyar sako matan, musamman ma kungiyar agaji ta Red Cross. A yau Talata ne ake sa ran ‘yan matan zasu gana da shugaba Buhari a fadar Aso Rock.