Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kawo Karshen Taron Bita Na Malaman Addinai A Kano


Taswirar Kwaryar Kano
Taswirar Kwaryar Kano

An kammala taron bita na yini guda ga malaman addinai a Kano da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya hadin gwiwa da cibiyar bincike da bada horo kan harkokin demokaradiyya dake gidan Mambayya a Kano suka shirya.

Mahalarta taron da suka kunshi malaman addinin musulunci da shugabannin Majami’u, su kimanin 50 da suka fito daga cikin da wajen Kano, sunyi musayar ra’ayi da fasaha kan rawar da jagororin addinan ke takawa wajen magance matsalolin rashawa da cin hanci a dukkannin matakai, da kuma wanzar da shugabanci na gari.

Jakadan sakataren harkokin wajen Amurka na musamman akan lamuran hulda da musulman duniya Mr. Shaarik Zafar, wanda ya jagoranci taron ya bayyana gamsuwa game da bayanai da lafazin jagororin addinan.

Farfesa Haruna Wakili dake zaman daraktan cibiyar Manbayya masu karbar bakuncin taron, yace Manbayya cibiya ce ta komai da ruwanka in dai ana magana ne kan batun shugabanci na gari.

Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG