A taron da suka gudanar domin bayyana rashin jin dadinsu dangane da yadda hukumomin zabe na jihohi ke bayyana jam'iyyun dake mulki a jihohin nasu a matsayin wadanda suka lashe zabukan da ake gudanarwa.
Shugaban jam'iyyar UPN Femi Paida a jihar Ogun yace ko kadan yadda jam'iyyun dake mulki a jihohinsu suke bayyana cewa su ne suka lashe zabuka bai dace ba. Yayi misali da zabukan da ka gudanar kwanan nan a jihar Ogun inda jam'iyyar APC mai mulki ta lashe zabukan da aka gudanar a kananan hukumomi ishirin na jihar da kuma na yakunan cigaban al'umma talatin da bakwai. Cikin kansiloli kuwa biyu kacal aka baiwa jam'yyar UPN da PDP mai kujera daya.
Kawar da hukumomin zaben jihohi zai taimaka wurin dorewar dimokradiya a Najeriya.
Otunba Paida yace matakan da ake dauka yanzu domin gudanar da zabuka basu dace ba don haka, majalisun tarayya su zauna su yi gyara a kundun tsarin kasar.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.