An kafa kotun sojan ne a ranar 9 ga watan Agusta shekara ta 2016, karkashin shugabancin Birgediya Janal Oji Adeniyi, wanda ya zartar da wannan hukunci ga jami’in sojan, kuma ya kasance hukunci na farko cikin irin kararrakin da suke da shi har guda 20 a gabansu.
Mai wakiltar sojan Najeriya a kotun ya karantawa kotun irin shari’ar dake gabansu, wanda daga bisani lauyoyin dake kare wanda ake zargi karkashin jagorancin Barista G. K. Abba sun roki kotun a rubuce don neman sassauci ga wanda ake yankewa hukuncin, ga abin da suka kira cewa “ya aikata abin da ya aikata ne cikin rashin sani”.
Sai dai kotun ta dan kebe a wani daki na musamman, inda ta tattauna akan irin hukuncin da za a zartar wanda daga bisani shugaban kotun ya bayyana hukuncin, inda yace kotu ta yanke hukuncin ‘daurin shekaru Uku a gidan yari kuma ta ragewa masa mukami a matsayinsa na sajant zuwa kurtu.
Tuni dai wannan kotu ta dage zamanta har zuwa ranar 20 ga wannan wata, wanda tace zata ci gaba da sauraron kararrakin nata da kuma yanke hukuncin karar dake gabanta.