Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rawar Da Malaman Addinai Ke Takawa Wajen Yaki Da Rashawa


Wakilin sakataren harkokin wajen Amurka na musamman akan harkokin hulda da musulmin duniya, Mr Shaarik Zafar, zai gabatar da jawabi ga taron malaman addinin musulinci dana Kirista a birnin Kano game da rawar da malaman ke takawa wajen yaki da rashawa a tsakanin al’umma.

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya da hadin gwiwa da cibiyar bincike da bada horo kan harkokin demokaradiyya dake gidan Mambayya a birnin Kano sune suka shirya taron. Inda aka zabo malamai da shugabannin Majami’u kimanin 50 a ciki da wajen Kano, domin halartar taron wanda zai mayar da hankali akan rawar da jagororin addinan zasu taka wajen magance matsalolin rashawa da cin hanci tare da wanzar da shugabanci na gari.

Gabanin taron Mr. Shaaarik Zafar, ya gana da manema labarai don karin haske kan rawar da ofishinsa ke takawa wajen inganta hulda tsakanin Amurka da Musulman duniya kimanin Biliyan Guda da Miliyan Dari Shida, Zafar yace a matsayina na jakadan musamman aiki na shine tallafawa gwamnatin Amurka da ma’aikatar harkokin wajenta ta fuskar mua’mula ko hulda da musulman duniya.

Kafin ya bar jihar Kano Jakada Zafar, ana sa ran zai gana da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da maimartaba sarkin Kano Mallam Sunisi Lamido, haka kuma ya tattauna da kungiyoyin fararen hula kan muhimman batutuwan da suka shafi lardin na Arewa.

Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG