Kotun dake unguwar Jaki cikin Bauchi babban birnin jihar Bauchi ya kasa zama domin matasan basu gamsu da irin shari'ar da ake yiwa masu yin luadi ba. Suna ganin hukuncin da kotun ke basu bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da laifin yin luadi da madigo.
Bisa ga duka alamu matasan na nuna rashin jin dadinsu da 'yan luadi da kuma yadda ake gudanar da shari'ar wadanda ake zargin yin luadi. Matasan dai sun shiga jifar kotun da duwatsu da kuma yin ikirarin shiga kotun.
Bayan an kwashe lokaci ana gwa-gwa-gwa da matasan jami'an tsaro sun yi anfani da barkonun tsohuwa da kuma harbi a sama domin tarwatsa matasan da kuma korarsu daga harabar kotun.
Kafin hayaniyar da matasa suka tayar sai da aka fafata tsakanin lauyan gwamnati da lauyan dake kare daya daga cikin wadanda ake zarginsu da laifin yin luadi wato Ibrahim Marafa shugaban makarantar sakandare ta gwamnati ta garin Mainamaji da ake zargin ya yi luadi. Matashin da aka yiwa bulala da tarar nera dubu biyar makon jiya ya ce Ibrahim Marafan ne ya sa shi hanyar luadi.
Barrister Kamdi Musa shi ne lauyan Ibrahim Marafa kuma kotun ta hanashi beli saboda ya yi anfani da kundun tsarin mulkin Najeriya ne maimakon dokokin tsarin Musulunci da kotun ke aiki da su.
A wani kotun cikin garin Bauchi yau ne za'a cigaba da shari'ar wasu mutane biyu da ake zarginsu da yin luadi.
Ga karin bayani.