Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa da a Ke Zargin 'Yan Luwadi ne Sun Fada Hannun Mahukunta a Jihar Bauchi


Kasa da mako daya bayan da shugaban kasar Najeriya ya sanya hannu kan dokar hana aure tsakanin jinsi daya,an kama wasu matasa da zargin 'yan luwadi ne a jihar Bauchi

A jihar Bauchi wasu matasa su goma sha biyu sun fada hannun hukumar shariar Musulunci wadda ta zargesu da cewa 'yan kungiyar luadi ne da doka ta haramta.

Hukumar Shari'ar Musulunci ta gurfanar da matasan su goma sha biyu gaban shari'a. Tana zarginsu cewa su 'yan kungiyar luadi ne. Matasan an kamasu ne a cikin wani otel dake cikin garin Bauchi. Alhaji Mustapha Shehu Illela shugaban Hukumar Shari'ar Musulunci ta jihar Bauchi ya ce za'a yiwa matasan goma sha biyu hukunci bisa ga yadda shari'ar Musulunci ta tanada. Ya ce al'ummar Bauchi suka ce suna son shari'ar Musulunci kuma shari'ar ta hana wannan muguwar dabi'a kuma tana da nata irin hukuncin . Allah ya tanadi tashi dokar kuma dokarsa za'a bi.

Shugaban addinin Musulunci Sheik Tahiru Usman Bauchi da kuma na kungiyar Kirista Rev Lauwi Popti sun ce addini ya la'anci mai yin laudi da madigo. Sheik Tahiru ya ce duk cikin dabbobin da Allah ya yi babu muguwar dabba kamar namuji dake luadi. Daurawa namuji da namuji aure wata muguwar shegantaka ce. Da mace ke auren mace da duniya ta kare. Wadannan abubuwa sabawa dokokin Ubangiji ne. Da namuji zai auri namiji wa zai haifu kuma. Duniya ta kare ke nan. Abun da Allah ya yi a barshi haka.Namuji ya auri mace. Amma addini bai yadda a yi luadi ko madigo ba.

A kiristance Rev Popti ya ce munmunan abu ne. Ya ce Littafi Mai Tsarki ya koya mana kada ma a anbaci luadi ko madigo a cikin jama'a domin suna da muni sosai. Luadi da madigo hali ne na dabba ba hali ne na mutum ba. Ya ce Ubangiji ya ce duk wadanda suke yin wadannan a fitar dasu domin basu da ceto kuma basu da aljanna.

Kwamandan Hisba a jihar Bauchi Alhaji J.D. Hassan ya ce cikin matasan 12 daya ne kawai Ibo. Amma matasan nada damar daukaka kara a kotun Musulunci kawai.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG