Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Hana Fyade, Madigo, Luadi da Cin Zarafin Mata a Kano


Britaniya shahzodasida Charlz yangi Zelandiyada Maori qabilasi liderlari bilan ko'rishmoqda
Britaniya shahzodasida Charlz yangi Zelandiyada Maori qabilasi liderlari bilan ko'rishmoqda

Yiwa mata fyade a Kano ya dauki wani salo lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta amince da dokar da majalisa ta kudura na hana fyade da cin zarafin mata ta kowace hanya.

Bayan hana fyade, daftarin dokar da majalisa ta kudura wadda gwamna ya sa hannu akai, ya kunshi wasu alamura da suka shafi luadi da madigo da al'adan nan ta tarawa da dabbobi da mutane kan yi.

Haka kuma dokar ta tabo batutuwan cin zarafin mata walau a makarantu ne ko wuraren aiki. Dokar tayi tanadin daurin rai da rai ko kuma daurin shekaru 14 da tarar nera dubu dari biyu ga duk wanda aka kama da laifin fyade.

Masu luadi da 'yan madigo da masu tarawa da dabbobi zasu fuskanci hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 14 da tarar nera dubu hamsin. Su kuma masu anfani da matsayinsu a makarantu da wuraren aiki wajen cin zarafi da musgunawa mata ta hanyar hanasu cin jarabawa ko samun gurbi a jami'a ko aiki ko hana ma'aikaciya cigaba a wurin aikinta dokar tayi masu tanadin daurin shekaru bakwai a gidan maza da tarar nera dubu hamsin.

Tuni al'ummar jihar suka fara tsokaci game da dokar. Wani yace matakin da aka dauka yayi daidai domin abubuwa sun baci yanzu ba babba ba yaro. Yarinya karama 'yar shekara hudu zuwa biyar sai a yi mata fyade. Wata kuma cewa ta yi dokar tayi mata daidai domin ko a wannan shekara an samu rahotannin fyade fiye da kima.

Masu fashin baki ma ba'a barsu baya ba. Aliyu Abubakar Getso dan jarida a Kano yace yunkurin majalisar abun yabawa ne duk da jinkirin da aka samu wajen kafa dokar idan aka yi la'akari da yawan fyade a jihar. Amma da an yi anfani da shari'ar Musulunci wajen magance abubuwan da dokar ta ayana. Matukar ba'a bi dokar Allah ba ana gidan jiya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG